Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau A Turkiya Wata Mota Shake da Bam Ta Kashe Mutane 11


Wurin da bam ya tashi a Turkiya

Wata mota dauke da bam da ta fashe a yau Juma’a a garin Cizre da ke kudu maso gabashin Turkiyya, ta yi sanadin mutuwar ‘yan sanda 11,a cewar jami’an asibiti.

Sun kuma kara da cewa wasu da dama sun jikkata sanadiyar harin.

Kafafan yada labaran kasar, sun nuna tashin hayaki bayan da aukuwar harin, a wurin da ake tunanin shingen bincike ne na ‘Yan sanda.

Harin na yau Juma’a ya faru ne da misalin karfe 6:30 a gogon yankin na Turkiyya, yayin da hukumomin kasar suka sha alwashin daukar fansa.

Shi dai wannan gari na Cizre da ke Sirnak, ya na kusa ne da wani Lardi da ke kan iyakar Syria da Iraqi, wanda mafi yawa Kurdwa ke zauna a cikin sa.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin wannan hari, amma kamfanin Dillancin labaran Anadolu, ya danganta harin da kungiyar PKK, wadda kungiya ce da aka saka ta a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ta da kayar baya.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG