Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou.
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou.

Shugaba Mohamed Bazoum ne ya jagoranci taron karrama mamacin, wanda ya rasu a ranar Litinin din da ta gabata, a fadarsa kafin a wuce da gawarsa zuwa makwancin karshe a garinsa na haifuwa wato Kornaka da ke Jihar Maradi. 

NIAMEY, NIGER - Daruruwan manyan jami’an hukumar Nijar da ‘jakadun kasashen waje, da na kungiyoyin kasa da kasa, ‘yan uwa da abokai, da iyalai ne suka hallara a farfajiyar fadar shugaban kasar Nijar da hantsin yau Alhamis 21 ga watan Yuli domin yi wa marigayi Sanoussi Jackou bankwanan karshe.

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou

Tsohon Firai Minista Dr. Hamid Algabid a lokacin da yake jawabi a gaban gawar Alhaji Sanoussi Jackou, ya na mai cewa: Sanoussi Tambari Jackou, fitaccen dan Nijar, ka cancanci samun dukkan wata karramawar da ta dace, ya kai Sanoussi, ka tafi ka bar mu. Ka rasu kana da shekaru 82 sakamakon rashin lafiya. Ka auri matarka Francoise a ranar 19 ga watan disamban 1964 a garin Didjon na kasar Faransa, kun haifi ‘ya’ya mata biyar, wadanda suka hada da Rakiatou Christelle da Hadiza da Maimouna da Safiatou da Nafi. Kana da jikoki 22, da tattaba kunne da dama. Sanoussi a lokacin da kake da rai, kai mutun ne jajirtacce mai son mutane.

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou

Shugaban kungiyar fafitika ta MPCR Nouhou Mahamadou Arzika wanda a wani lokaci wasu ke kallonsa tamkar wani magajin Sanoussi Jackou a kan maganar fede gaskiya komai dacinta, shi ma ya yi bayani akan halayyar wannan fitaccen dan siyasa.

Tsohon Ministan hadin kan kasashen Afrika, tsohon Minstan ilimi mai zurfi, wanda ya wakilici al’umma a majalissar dokokin kasa sau tari, ba’idin aikinsa na malamin jami’a, mutuwar wannan tsohon masanin tattalin arziki kuma dan gidan sarautar Kornaka babban rashi ga jama’ar Nijar ne.

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou

A tsawon rayuwarsa Sanoussi Jackou ya bakunci gidan yari sau 26 saboda dalilai masu nasaba da fadin albarkacin baki inda a wani lokaci ya shafe shekaru kusan 12 garkame a kurkuku a zamanin gwamnatin mulkin Colonel Seini Kountche.

Ya rubuta litattafai da dama ya kuma kafa jaridu masu zaman kansu a kalla uku wadanda suka hada da La Roue de l’Histoire da l’Arbre a Palabre da le Sens de l’Histoire.

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou
Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou

A karshen taron karammawar da aka shirya a hukunce domin marigayi Sanoussi Jackou dimbin jami’ai da makusanta daga nan Yamai sun yi masa rakiya zuwa garin Kornaka inda aka yi jana’izarsa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Yau Aka Yi Jan’izar Fitaccen ‘Dan Siyasar Jamhuriyar Nijar Sanoussi Tambari Jackou.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

XS
SM
MD
LG