Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Bikin Ranar Yaran Afirka


Wasu yara a Afirka

A kowace shekara, ana kebe ranar 16 ga watan Yuni domin duba da nazarin darajar yara a Afirka da kuma mayar da hankali kan wasu abubuwa da suka danganci yaran.

An kirkiro wannan ranar ne domin tunawa da wasu yara 'yan Soweto wadanda aka kashe bayan da suka fito zanga-zanga kan alhinin tsarin karatu mai nuna wariya a ranar 16 ga watan Yuni na shekarar 1976.

Tsohuwar kungiyar hadin kai a Afirka ta OAU ce ta kirkiro wannan ranar.

Kungiyoyi masu zaman kansu kan zauna a wannan ranar domin nazarin 'yancin yara da ba sa samun karatu kyauta da kuma yadda za a habbaka ilimi.

Yayin da duniya ke murnar zagayowar ranar a wannan shekarar, shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sha alwashin mayar da hankali kan kare yara daga fyade, da duk wani nau'i na cin zarafi.

Shugaban ya jadadda yadda gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar cewa duk yara sun sami zuwa makaranta mai kyau ta hanyar samar da ilmi kyauta a shekaru tara na farko a rayuwarsu.

Kana, shugaban ya nuna damuwarsa kan karuwar lamuran fyade kan yara mata a cikin kwanakin nan.

A kan hakan ya umarci dukkanin gwamnatoci a kasar da su kara kaimi wajen taimakon da ake baiwa yaran da suka tsince kansu cikin wannan lamarin, da kuma kama wadanda ke aikata wadannan miyagun laifuka.

Shugaban ya ce kare dukannin yara a Najeriya daga fyade da cin zarifi, da kuma tabbatar cewa sun samu yanayin koyo da girma mai inganci 'yancinsu ne.

A cewar alkaluma milliyoyin yara a Afirka basa zuwa makaranta saboda yadda ake fama da talauci a yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG