Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Yi Wa George Floyd Ban Kwana


Wata mata a gaban zanen hoton George Floyd.
Wata mata a gaban zanen hoton George Floyd.

A yau Talata dangi da abokai su ke yiwa George Floyd bankwana na karshe a tsare-tsaren jana’izarsa da za a yi a birnin Houston, makwanni biyu bayan mutuwarsa a hannun ‘yan sanda, abin da ya sake ta da zanga-zanga a birane da dama na Amurka na nuna kyamar wuce gona da iri da ‘yan sanda suke yi.

Bayan addu’oin, ‘yan sandan birnin Houston za su yi jerin gwano su raka tawagar zuwa birnin Pearland inda za'a binne Floyd a kusa da kabarin mahaifiyarsa.

An kunna wutar zauren majalisar birnin a daren jiya Litinin da launin ruwan kwai da zinari, kalar makarantar da Floyd ya yi, domin tunawa da rayuwarsa.

Sauran birane sun bi sahu da kunna wuta da wadannan launuka da suka hada da biranen Los Angeles, Boston, Oakland, Las Vegas, New York da sauransu.

An ba sauran jama’a damar karrama Flyod ta karshe jiya Litinin inda dubban mutane suka yi tururuwa a majami’ar Praise, wurinda aka bude akwatin gawarshi.

An kuma yi addu’oin tunawa da shi a biranen Minneapolis da kuma Raeford.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG