Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Zabe a Mali, Gobe Kuma a Zimbabwe


Mata ma ba a bar su a baya ba a zaben na Mali

An shiga kakar zabuka a nahiyar Afirka, inda a yau ake yi a kasar Mali, gobe a Zimbabwe nan gaba kadan kuma a Kamaru da Kongo da dai sauransu. Wannan na faruwa a daidai lokacin da ake samun rahotannin murkushe madafun dimokaradiyya a kasashe da dama.

Yau 'yan kasar Mali ke kada kuri'ar yanke shawarar ko su bai wa Shugaba Ibrahim Bubakar Keita wa'adi na biyu ko a'a. Su kuma 'yan kasar Zimbabwe harama su ke ta kada tasu kuri'ar a gobe Litini a zabensu na farko tun bayan da dadadden Shugabansu Robert Mugabe ya sauka karfi-da-yaji a watan Nuwamba.

Batun ko jama'a za su amince da sahihancin sakamakon wadannan zabukan - da ma karin wasu na kasashen Afirka Kudu da Sahara akalla biyu cikin 'yan watanni masu zuwa -- ciki har da wanda za a yi a kasar Kamaru a watan Oktoba, da Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo a watan Disamba - duk wannan ya danganta ne ga yadda jama'ar su ka fahimci zabukan.

Ingancin zabukan dai ya danganta ne ga yadda masu tsarawa su ka yi. A kasar Mali hukumomi uku ne ke da ruwa da tsaki wajen fasalta tsarin zabe. A kasar Zimbabwe kuwa Hukumar zabe mai zaman kanta ce kawai ke tsarawa.

Tuni rahoton kungiyar saka ido kan sahihancin zabe ta Freedom House ta ce a kasashe da dama, an ga karuwar murkushe madafun dimokaradiyya ta fuskoki dabam-dabam.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG