Accessibility links

Yau Ake Zaben Shugaban Kasa A Australiya

  • Ibrahim Garba

Shugaban Australiya Kevin Rudd

Yau Asabar ake zaben Shugaban kasa a kasar Australiya, inda ake ganin da kyar gwamnati mai ci ta su Firayim Minista Kevin Rudd ta kai labarai.

‘Yan kasar Australia za su yi babban zabensu a yau dinnan Asabar, inda ake kyautata zaton za su maido da masu ra’ayin rikau bisa gadon mulki, su kawo karshen mulkin jam’iyyar ‘Yan Kwadago (ko Labor Party) mai tsawon shekaru 6.

Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya bayan nan ya nuna cewa Tony Abbott na jam’iyyar Liberal-National Party ya dara Firayim Minista Kevin Rudd na Labor Party.

A ranar da aka kammala yakin neman zabe, wato jiya Jumma’a, Mr. Rudd ya yi kira ga ‘yan Kasar ta Autralia da kar su fidda da tsammani kan nasararsa saboda ya na ma iya yin galaba a ranar zaben.

Zaben ya zo ne watannin uku kawai bayan da Mr. Rudd ya maye gurbin Firayim Minista mace ta farko a Australia Julia Gillard, a wani yinkuri na kara farfado da farin jinin jam’iyyar kafin babban zaben.

Batutuwan da aka fi la’akari da su a zaben sun hada da makomar tattalin arzikin kasar, da maganar bakin haure da kuma canjin yanayi.
XS
SM
MD
LG