Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Alhamis Za'a Sake Gudanar da Zaben Shugaban Kasar Kenya


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta yana yiwa magoya bayansa jawabi

A yau Alhamis za a gudanar da zaben shugaban kasar Kenya kamar yadda aka shirya, bayan da kotun kolin kasar ta gaza sauraron karar da aka shigar akan neman a ‘dage zaben.

A cewar shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kenya, Wafula Chebukati, “Bisa ga tabbacin bayanan da wasu hukumomi da jami’an tsaro suka gabatarwa da hukumar, za a gudanar da zabe yau Alhamis 26 ta watan Oktoba kamar yadda aka tsara.”

Amma shugaban jam’iyyar adawar Kenya, Raila Odinga, wanda ya janye kansa daga zaben a farkon watannan, ya yi kira ga magoya bayansa a jiya Laraba da su kauracewa zaben.

Da safiyar jiya Laraba ne babban alkali kasar David Maraga, ya fada cewa alkalai biyu ne kadai suka je kotun cikin alkalai bakwai da ake da su, hakan ya gaza adadin alkalai biyar da ake bukata don yanke hukunci.

Haka kuma wani alkali yace nade-naden jami’an hukumar zaben da aka yi don zaben na yau, ba a yi su bisa ka’ida ba.

Sai dai kuma hukumar zaben ta Kenya ta ce nade-naden na bisa ka’ida, kuma jami’an zasu gudanar da harkokin zaben shugaban kasar na yau.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG