Accessibility links

Yau an rantsar da Shugaban wuccin gadin Mali


Shugaban juyin mulkin Mali Amadou Sanogo kenan ke mubaya'a ga sabon Shugaban wuccin gadi Dioncounda Traore, yau din nan a birnin Bamako

A yau Alhamis aka gudanar da bikin rantsar da kakakin

A yau Alhamis aka gudanar da bikin rantsar da kakakin majalisar dokokin kasar Mali Diocounda Traore, a zaman sabon shugaban kasa.

Tsarin mulkin kasar Mali ya baiwa Mr. Traore tsahon kwanaki arba’in da ya shirya sabon zabe.

Rantsar da sabon shugaban na kasar Mali na daga cikin shirin yarjejeniyar maida mulki hannun farar hular da aka cimma tsakanin (ECOWAS) da sojin da suka yi jagorancin hambaras da Gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Shugaba Amadou Toumani Toure.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG