Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Zata Tura Sojoji Zuwa Mali Da Guinea-Bissau


Wasu jami'an da ba a bayyana sunayensu ba sun ce za a tura sojoji dubu 3 zuwa Mali, yayin da za a tura 600 zuwa Guinea-Bissau domin sanya idanu kan maido da mulkin farar hula.

Kungiyar Tarayyar tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta ce zata tura sojoji zuwa Mali da Guinea-Bissau domin sanya idanu kan yadda za a mayar da kasashen biyu turbar mulkin farar hula bayan juye-juyen mulki.

A wurin wani taron koli na musamman alhamis a kasar Ivory Coast, kungiyar ECOWAS ta ce ya kamata kasashen biyu su shirya gudanar da zabubbukan majalisun kasa da na shugabanni a cikin shekara daya. Ta yi barazanar kafa takunkumi idan har shugabannin juyin mulkin suka yi kokarin makalewa a kan mulki.

Kafofin yada labarai sun ambaci jami’an da ba a bayyana sunayensu ba su na fadin cewa za a tura sojojin ECOWAS har dubu 3 zuwa kasar Mali, inda a watan da ya shige sojoji suka yi bore suka hambarar da shugaban kasar da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.

Ana sa ran tura sojoji kimanin 600 zuwa kasar Guinea-Bissau, inda sojoji suka kwaci mulki ranar 12 ga watan Afrilu, makonni kadan kafin a gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG