Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Asabar Cain zai yi sanarwa game da yakin neman zabensa


Dan takarar shugabancin Amurka Herman Cain

Dan takarar Shugaban kasar Amurka a karkashin jam’iyyar Republican

Dan takarar Shugaban kasar Amurka a karkashin jam’iyyar Republican Herman Cain, ya ce zai bayar da sanarwa game da makomar yakin neman zabensa a yau Asabar.

Yakin neman zaben shugaban kasan na Cain dai ya yi ta gamuwa da cikas saboda jerin zargin da ake masa na lalata da kuma soyayya da wata mata na tsawon shekaru 13 a jiharsa ta haihuwa wato Georgia.

To amman shi wannan tsohon shugaban kamfanin pizza din ya karyata zargin, to amman ya ce zai sake yin nazarin yakin neman zaben nasa. Cain na shirin bayar da sanarwar ce daga babban birnin jihar wato Atlanta. Ya iso ranar Jumma’a don ya hadu da matarsa su tattauna kan al’amarin

Cain ya dare kwaloluwar mizanin kwarjinin ‘yan takara a karkashin jam’iyyar Republican a cikin watan Satumba da Oktoba, to amman magoya bayansa sun ragu matuka tun bayan da zarge-zargen su ka bullo.

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG