Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Cutar Dajin Jini Ta Duniya


Dr. Andiya Abdulkadir likitan cutar dajin jini

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta kebe domin tunawa da cutar dajin jini da kan kashe mutum idan ba'a sani ba kuma ba'a dauki matakin warkar dashi ba cikin gaggawa

Wata da cutar ta kama a jamhuriyar Nijar Hajiya Safiya tace da ciwon ya kamata kasala ce da ciwon gabobi ta soma ji amma da aka yi bincike aka gano tana da cutar, tunda ta soma shan magani ta soma samun sauki.

Cutar dajin jini ta dade kuma likitoci sun bayyanata a matsayin cutar da ke yiwa rayuwar mutum barazana idan ba'a shawo kanta ba da wuri. Sannu a hankali cutar ke rage jinin wanda ta kama saboda gurbacewar kayoyin halittar jini a jikin mutum.

Dr. Andiya Abdulkadir likita ne dake kula da masu cutar dajin jini kuma yayi bayani. Yace jinin dake cikin mutum adadinshi cikin jiki wata ukku ne kawai. Bayan wata ukku sai halitta ta sake kirkiro da sabon jini. Yace matsalar itace cutar cikin bargo take shiga inda take hana kirkiro da halittar dake sabunta jini. Duk wanda cutar ta kama sai an sake mashi bargo a kasar turai domin ba'a yi a Afirka. Yace babu wanda baya iya kamuwa da cutar musamman daga wayar salula. Maganin cutar yana da tsada ainun.

A Nijar mutane sama da dari biyu ne aka gano suna da cutar. Malam Aliyu Bukari na kungiyar masu fama da cutar ya koka akan yadda ake wahalar dasu kafin magani ya shiga hannunsu.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG