Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Hada Mangunguna Ta Duniya


Magungunan da aka hada

Yau ce ranar masu harhada magunguna ta duniya, inda kwararru da sauran masu ruwa da tsaki a wannan fanni ke gangamin wayar da kan jama’a game da rawar da suke takawa wajen kiwon lafiyar bil’adama.

An fara bukukuwan ranar ce a watan Satumba na shekara ta 2010, bayan da a shekara ta 2009, taron koli na kungiyar masu harhada magunguna ta duniya, international Pharmaceutical Federation ya amince da kebe ranar 25 ga Satumbar kowace shekara domin gudanar da wannan gangami.

Wannan rana ta 25 ga Satumba ta yi dai-dai da ranar da aka kafa kungiyar a shekarar 1912, mai hedkwata a kasar Netherlands wacce a yanzu kuma ke da fiye da mambobi miliyan a kasashe 139 na duniya

Nigeria dai ta bi sahun kasashen duniya wajen gudanar da wannan gangami karo na 9.

Pharmacist Bala Maikudi, shugaban kungiyar masu fasahar harhada magunguna ta Najeriya reshen jihar Kano ya fayyace abubuwan da suke Muradin cimmawa.

Yace “ abun da muke so shi ne mutane su san wanene mai hada magani? Menene hada magani ya keyi? Ina zaka samu mai hada magani? Wace shawara zaka nema daga gareshi?”

Abu da ya kawo tambayoyin shi ne yawar da masu hada maganin suka yi yanzu lamarin da ya sa yanzu mutane sun fara sanin wanene mai hada magani kuma ya wuce haka saboda shi yake gano maganin, ya hadashi ya kuma sarafashi. Bala Maikudiyace mai hada maganin ya fi kowa sanin maganin.

Ya yin da masu harhada magunguna ke kokarin ganin al’umma sun fahimci muhimancin rawar da suke takawa wajen kiwon lafiyar bil’adama, a Kano an kwashe lokaci mai tsawo ana kai ruwa rana tsakanin hukumomin jihar da kungiyar dillalan magunguna.

Tun a shekara ta 2012 ne gwamnatin Kano ta dauki matakin fitar da dillalan daga kasuwar Sabon Gari saboda zargin suna sayar da magunguna marasa inganci da wadanda ke sanya maye alamarin da ta ce yana kara yawan masu ta’ammali da kwayoyi a birni da kewayen Kano.

Alhaji Hussaini Labaran Zakari shugaban reshen jihar Kano na kungiyar dillan magunguna ta kasa ya ce sun fada cewa idan sun ba da labara mahukunta su kama su dauki mataki mai tsanani akan masu ta’ammali da kwayoyi. Idan kuma su masu sayar da magunguna ne suka ga wata illa suka dauki mataki a kai mahukumta su goya masu baya.

Yanzu haka dai wani kamfani tare da hadin gwiwa da gwamnati na aikin gina sabuwar kasuwa ta masu hada hadar magunguna zalla a Kano a wani mataki na sanya ido sosai akan yadda suke tafiyar da harkokin su.

A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG