Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Samun Bayanai Ta Majalisar Dinkin Duniya


 Antonio Guterres Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya
Antonio Guterres Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

A shekarar 2015 hukumar UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta amince da ranar 28 ta kowane watan Satumba a matsayin ranar samun bayanai ta duniya

Hukumar EUNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta amince da tsayar da kowace ranar 28 din watan Satumba a matsayin ranar samun bayani ta duniya.

A wannan shekarar an fara bikin rananr ne tun rana 25 ta wannan watan wanda yake gudana a kasar Tunisia, kasar da aka ce yanzu haka dai ta fi kowace kasa mai tasowa hanyoyin samun bayanan gwamnati.

Najeriya na cikin kasashen duniya da aka tsayar da dokar samun bayanan gwamnati ko kuma jami'an tsaro.To sai dai ba kasafai ba ne jami'an gwamnati ko na tsaro ke bin umurnin kotu ba dangane da bada bayanai.

Sau tari hakan 'yan jarida ko lauyoyi na samun bayanai daga hukumomin gwamnati ba ya cimma ruwa.

Dr Danlami Alhassan kwararre kan harkokin sadarwa na Jami'ar Bayero dake Kano yace da yake 'yan jarida ma basu ba ranar wani mahimmanci ba ta hanyar yin gangami ko shirya kasidu hukumomin gwamnati su kan ki su bada rahoton da ake nema.

'Yan jarida na fuskantar matsaloli a Najeriya wajen tara bayanai saboda dari dari da jami'an gwamnati keyi da 'yan jarida. Idan kuma su jami'an gwamnatin suna wata muna-muna ba zasu so bada bayani ba.

Dr. Danlami Alhassan ya bayyana abun da dokokin bada bayanai suka kunsa.

Yana mai cewa na daya duk wani dan kasa nada 'yancin ya nemi bayani daga gwamnati ba tare da gindiya masa wasu sharuda ba. Na biyu an ba dan kasa ya je kotu ta tilastawa ma'aikatar gwamnati bada bayanan da mutum ke nema.

Abu na uku akwai hukumcin daurin shekara daya ga duk jam'in gwamnatin da yaki bada bayanan da ake nema. Abu na hudu duk wani jami'in gwamnati da ya ga ana almundahana ya kuma bayyanawa jama'a doka ta kareshi daga duk wani hukumci.

Doka kuma ta ce cikin kwana bakwai a baiwa mutum bayanan da ya bukata, idan kuma ba'a bayar ba to a bada cikakken bayanin dalilin da ya sa ba'a yi ba cikin kwanaki bakwan.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG