Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Ranar Tunawa Da Martin Luther King a Amurka


Dr.Martin Luther King Jr
Dr.Martin Luther King Jr

Yau a duk fadin Amurka ake hutun tunawa da jagoran gwagwarmayar kwato wa bakake da tsiraru cikakken 'yancin zama amurkawa, wato Martin Luther King Jr. cikin zanga zangar lumana

A yau Litinin ne Amurkawa ke bikin girmama Martin Luther KING Jr., mutumin da ya jagoranci gwagwarmayar kwato ‘yanci da hakkokin bakar fata da ‘yan tsiraru, wanda kuma yayi imani da cewa nasarar irin wannan gwagwarmayar ta ta’allaka ne kan gudanar da ita cikin lumana.

A kowacce shekara, a ranar Litinin ta uku a watan Junairu, Amurkawa na girmama shugaban ‘yancin bakar fatan da aka kashe, wanda a shekarun 1950 da 1960 ya shirya tare da jagorantar kyamfe na nuna kyamar wariyar launin fata dake aukuwa a jihohin kudancin Amurka da kuma yakin neman daidaito tsakanin fari da baki da kuma ‘yancin zabe.

Mutane da yawa a fadin Amurka suna yin hutun tuna ayyukan da gwarzon ya yi na kawo karshen wariyar launin fata ta hanyar yin ayyukan gayya na taimakon al’umma. Majalisar Dokokin Amurka ta girmama shi Martin Luther King a shekarar 1994 ta hanyar kebe wannan rana a zaman ta yin hidima ga kasa.

Shugaba Donald Trump ya yi bayani akan jarumin a wani zama da aka yi a birnin Washington ranar Jumma’ar data gabata inda ya yabeshi da ayyukanshi na zanga zangar lumana na neman daidaito da kwanciyar hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG