Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ce Zagayowar Ranar Dimokradiya A Najeriya


Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Ranar 29 ta watan Mayun Shekarar 1999 Najeriya ta koma mulkin dimokradiya daga mulkin soja kuma tun daga lokacin aka ayyana ranar a matsayin ranar Dimokradiya wadda kowace shekara ake tunawa da zagayowarta kamar yadda ake yi yau a duk fadin kasar

A Najeriya ranar 29 Watan Mayu ne ake bukuwan ranar zagayowar komawa ga mulkin Dimokradiya a kasar.

A wani gefen kuma gwamnatin APC a karkashin shugabancin Muhammad Buhari ta cika shekaru uku cur tana mulkin kasar. Gwamnatin tasa tana samun yabo daga wasu ‘yan Najeriya dake ganin ta taka rawar gani, musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa da fatattakar ‘yan kungiyar Boko Haram dake tada kayar baya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Amma ‘yan babbar jam’iyyar adawa ta PDP suna ganin babu wani abun a zo a gani da gwamnatin APC din ta tsinana cikin shekaru ukun da tayi tana mulki.

To saidai gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce su aikin raya kasa suka sa agaba ba maganar jam’iyyar PDP ba.

Gwamnan na jahar Nija yace ba maganar wata jam’iyya ko ma PDP, jam’iyyar da ya ce ta mulki Najeriya na tsawon shekaru 16. Ya ce shi kansa ya yi PDP din. Sun san irin dukiyar da aka samu a can baya da irin almubazarancin da aka yi. Gwamnan ya ce da gwamnatin shugaba Buhari bata zo ba da watakila ma yanzu babu kasar saboda irin mawuyacin halin da kasar zata shiga.

Duk da furucin gwamnan, jam’iyyar ta PDP ta ce tana ganin haske a gaba dangane da babban zaben badi kamar yadda shugaban jam’iyyar na jihar Neja Barrister Tanko Beji ya fada. Y ace sun yi na’am da irin goyon bayan da jama’a ke basu. Yanzu dai ana jiran lokaci ne kawai.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Btsari da karin bayani

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG