Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Juma'a Shugaban Amurka Ya Nufi Kasar Vietnam


Shugaba Trump yayinda yake barin China zuwa Vietnam
Shugaba Trump yayinda yake barin China zuwa Vietnam

Shugaban Amurka Donald Trump ya nufi kasar Vietnam a yau Juma’a, a ziyarar kwanaki 12 da yake yi a gabashin Asiya, inda ya yake tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasuwanci da diplomasiyya da kuma Korea ta Arewa.

Trump zai ziyarci kasar Vietnam ne, domin halartar taron koli na kungiyar hadakar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya na APEC, inda ake sa ran manyan shugabannin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a yankin, za su tattauna kan bunkasa da kuma hadin kan kasashen yankin.

Yayin wannan ziyara, Trump zai hadu ya kuma gaisa da tsoffin sojojin Amurka da ke zaune a kasar ta Vietnam.

A daya bangaren kuma, ya zuwa jiya Alhamis, babu tabbacin ko ganawa tsakanin shugaba Trump da takwaran aikinsa na Rasha Vladmir Putin za ta yiwu ko a’a.

Jami’i a Fadar Kremlin, Yury Ushakov ya fadawa kamfanonin dillancin labaran kasar Rasha cewa shugabannin biyu za su hadu a yau Juma’a a gefen taron na APEC, wanda da zai gudana a Danang.

Sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya nuna shakkun yiwuwar haduwar shugabannin, yana mai cewa babu wani abu da ya nuna ko an samu ci gaba kan muhimman batutuwan da ke tsakanin kasashen biyu, da har za su sa shugabannin su hadu gaba-da-gaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG