Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Kotun Kolin Amurka Zata yanke shawara Ko Shugaban Amurka Na Da Ikkon Takaita Shigar Mutane Kasar


Shugaban Amurka, Donald Trump

Kotun kolin Amurka zata yanke shawara akan ko shugaban Amurka nada ikkon takaita shiga kasar daga wasu kasashen da akasarin 'yan kasarsu Musulmi ne, kasashe irinsu Libya, Yemen,Somalia, Syria, Koriya ta Arewa da Venezuela

A yau Laraba, kotun kolin Amurka za ta saurari muhawara kan ko shugaba Donald Trump, zai iya takaita shigar matafiya cikin Amurka, wadanda suka fito daga wasu kasashe, wadanda mafiya yawansu na Musulmi ne.

Kasashen sun hada da Iran, Libya Korea ta Arewa, Syria, Venezuela, Somalia da kuma Yemen.

Tun bayan da ya hau kan karagar mulki, Trump ya fitar da tsare-tsarensa na shige da fice a kasar.

Matakai biyu da ya dauka kan haka na baya-baya, an aiwatar da su ne a mataki na wucin gadi, yayin da mataki na karshe-karshen nan ba shi da ranar karewa.

Jihar Hawaii da kungiyar Musulmin jihar da wasu mutane uku ne suka shigar da karar, ana kuma sa ran za su gabatar da bahasinsu, wanda zai kalubalanci matakin haramtawa wasu ‘yan kasashen waje shiga Amurka, a matsayin wani mataki na nuna wariya ga al’umar Musulmi, sannan za su nuna cewa shugaba Trump ya wuce gona da iri a harkokin shige da fice.

A daya bangaren, ana sa ran lauyoyin gwamnati za su nuna cewa shugaban yana da hurumin daukan wannan mataki kan shige da fice.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG