Accessibility links

Hukumar zaben Misra ta ce da karfe 3 na rana agogon kasar ne shugaban hukumar, Faruk Sultan, zai bayyana ko wanene yayi nasara a zaben fitar da gwani na shugaban kasa

A yau lahadi al’ummar Misra zasu ji kowanene shugaban kasarsu, kwanaki 500 cur a bayan da suka kori Hosni Mubarak daga kan wannan kujera a farko-farkon tunzurinsu na watan Fabrairun 2011.

Ana zaman tankiya sosai yayin da sakatare-janar na hukumar zabe ta Misra, Hatem Bagato, ya bayyana a jiya asabar cewa yau lahadi da karfe 3 na rana agogon kasar, shugaban hukumar zabe Faruk Sultan, zai bayyana sunan wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Dubban Misrawa sun gudanar da gangami jiya asabar da maraice a tsakiyar birnin al-Qahira domin bayyana goyon baya ga dan takararsu a cikin biyun da suka yi takara, watau Mohammed Morsi na jam’iyyar Ikhwanul Muslimun da tsohon firayim minista Ahmed Shafiq.

Magoya bayan Ikhwanul Muslimun sun ci gaba da yin gangami a dandalin Tahrir na al-Qahira, cibiyar tunzurin da aka fara watanni 16 da suka shige, su na bayyana goyon bayansu ga Morsi, yayin da su kuma magoya bayan Shafiq suka yi nasu gangamin a kusa da kushewar Dogonyaro.

An shirya bayyana sakamkon zaben tun ranar alhamis, amma sai hukumar zae ta ce tana bukatar karin lokaci domin binciken zargin aikata magudin da dukkan ‘yan takarar biyu suka yi.

Ko ma dai wanene zai zamo shugaban kasar, zai kasance ba ya da cikakken ikon da ‘yan takarar suka yi tsammani tun farko a lokacin da sojoji suka yi alkawarin mika mulki ga farar hula a ranar 1 ga watan Yuli.

A makon jiya, majalisar koli ta mulkin soja ta dauki wasu matakan kara jaddada ikon sojoji a kasar, ciki har da rushe majalisar dokokin da masu kishin Islama suka mamaye bisa umurnin wata kotu. Har ila yau majalisar ta ayyana wani sabon kundin tsarin mulki na wucin gadi wanda ya ba hafsoshin soja da kuma kotuna ikon yanke shawara ta karshe a kan akasarin manufofin hulda da kasashen waje da na cikin gida da kuma zaben wadanda zasu rubutawa kasar sabon tsarin mulki na dindindin.

XS
SM
MD
LG