Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin ake zaben shugaban kasa da na majalisu a Philippines


Magajin garin Davao, Rodrigo Duterte, dan takarar shugaban kasa dake kan gaba a zaben yau

Yau Ltinin al'ummar kasar Philippines suke zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun kasar

Shugaban kasar Philippines dake kan gado yanzu Benigno Aguino ya kira al'ummar kasar su tabbatar sun gudanar da zaben na yau lami lafiya ba tare da tada hargitsi ko wata tashin tashina ba.

A zaben na yau ne al'ummar kasar zasu zabi shugaban da zai maye gurbin Shugaba Benigno Aquino.

Tashin tashina da yin magudi lokacin zabe a kasar ta Philippines ba sabbin abu ba ne. Saidai shugaba Aquino ya gayawa al'ummar kasar cewa lokaci ya yi da zasu nunawa duniya, kasar ta san yadda ake gudanar da dimokradiya.

Yace "duk da son da muke yiwa 'yan takaranmu muna iya gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana".

Ra'ayoyin mutane da aka dauka gabanin zaben na yau na nuni da cewa Magajin Garin Davao wato Rodrigo Duterte wanda ya yi kamarin suna wajen furta kalamu masu bada tsoro, shi ne kan gaba. Duterte dai an sanshi da yin kalamun batanci da marasa da'a kan kwamnatin kasar. Shi ne kuma dan takara daya tilo da ya yi barazanar kashe masu aikata manyan laifuka.

Amma masu hamayya da Duterte da suka hada da shugaba Aquino sun ja kunnuwan jama'a kada su mika kasar wa wanda suka ce yana iya zama ma mulkin kama karya kafin a ankara.

A zaben na yau al'ummar kasar zasu zabi 'yan majalisun tarayya da na kananan hukumomi 18,000.

Kundun tsarin mulkin kasar ya ba shugaban kasar wa'adin mulki daya ne na shekara shida kawai.

Shugaban na yanzu Aquino ya sa kasar ta zama mai karfin tattalin arziki a yankin Asiya.

Amma masu hamayya dashi sun ce arzikin kasar na hannun wasu kalilan ne masu masana'antu tare da zargin cewa akwai rata baba tsakanin attajirai da talakawa.

XS
SM
MD
LG