Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Litinin Ce Ranar Maleriya Ta Duniya


Sauro, mai yada cutar maleriya
Sauro, mai yada cutar maleriya

An kebe wannan rana ta 25 Afrilu musamman dominn karrama kokarin yaki da wannan cuta a fadin duniya

Yau 25 ga watan Afrilu ta ke Ranar Maleriya ta Duniya.

Maleriya dai wata mummunar cuta ce da sauro ke yadawa, wadda kuma ta kan kashe kimanin mutane miliyan guda a fadin duniyar nan a kowace shekara.

Taron Duniya kan Kiwon Lafiya, shi ne ya assasa Ranar Maleriya ta Duniya a cikin shekarar 2007 don tunawa da kokarin da ake yi a fadin duniyar nan na kawar da cutar.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutanemiliyan dubu uku da dari uku ne a 2009 – wato kimamin rabin yawan mutanen da ke cikin duniyar nan -- su ka fuskanci barazanar yiwuwar kamuwa da maleriya.

Hukumar ta Lafiya ta Duniya ta ce mutanen da ke zaune cikin kasashe mafiya talauci, su ne su ka fi kasancewa cikin hadarin. Hukumar ta ce a kowace shekara akan sami masu kamuwa da maleriya wajen miliyan 250.

Kungiyar agajin likitoci ta kasa da kasa da ake kira “Doctors Without Borders” ta ce maleriya ce ta fi kashe yara ‘yan kasa da shekaru biyar a kasashen Afirka da ke kudu da Sahara. Hukumar ta lafiya ta ce ya kamata kasashen dasu ka ci gaba su himmantu a kullum ga taimakawa kasashe masu tasowa wajen yaki da maleriya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG