Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikakken Bayanin Cutar Maleriya Kashi Na Hudu - Alamun Cutar Maleriya


Jinjirin sauro

Alamun cutar Maleriya su na fara bullowa kwanaki 10 zuwa 15 a bayanda sauro mai dauke da wannan cuta ya ciji mutum, kuma sun hada da zazzabi da ciwon kai da kasala da kuma haraswa

Cutar Maleriya cuta ce ta zazzabi mai tsanani. Ana fara ganin alamunta akasari kwanaki 10 zuwa kwanaki 15 a bayan da sauro mai dauke da kwayar cutar ya ciji mutum. Alamun farko na wannan cuta, watau zazzabi, ciwon kai, jin sanyi da kuma haraswa, ba su yin tsanani, kuma da wuya a lokacin a gane cewa cutar Maleriya ce. Idan har ba a samu magani cikin awa 24, ko kwana daya ba, cutar Maleriyar da kwayar cutar Plasmodium Falciparum ta janyo zata yi tsanani har ma ta kai ga mutuwa.

Kananan yara a wuraren da wannan cuta ta zamo ruwan dare, su na nuna alamun wasu daga cikin wadannan cuce-cucen: kasala mai tsanani, wahalar numfashi dake tattare da rudewar ciki, ko kuma Maleriya mai kama bargon kashin baya. Haka su ma balagaggu ana ganin alamun cutar a wasu sassa da dama na jikinsu.

Idan jinsunan kwayar cutar Maleriya na Plasmodium Vivax ko Plasmodium Ovale ne suka kama mutum, to tana yiwuwa zazzabin ya sake dawo masa makonni ko watanni bayan na farko, koda kuwa mutumin ya fice daga inda ake da wannan cuta ta Maleriya. Dalilin wannan shi ne wadannan jinsunan kwayar cutar Maleriya biyu, su na iya zama su fake a cikin hantar mutum, kuma idan har ana son a warkar da mutum baki daya, to tilas a ba shi maganin da zai kawar da wadannan kwayoyin cuta masu buya cikin hanta.

Jinsunan kwayar cutar Maleriya na Plasmodium Falciparum da Plasmodium Malariae su ba su fakewa a cikin hantar dan Adam.

Duba Kashi Na Daya Na Cikakken Bayani Kan Cutar Maleriya

Duba Kashi Na Biyu Na Cikakken Bayani Kan Cutar Maleriya

Duba Kashi Na Uku Na Cikakken Bayani Kan Cutar Maleriya

XS
SM
MD
LG