Kungiyar Agaji Ta Red Cross Ta Kasa da Kasa da kuma jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce yau Jumma’a, tawagogin motocin da ke dauke da kayan agajin da ake matukar bukata, sun fara isa yankin gabashin Ghouta da aka mai kawanya, to amma sun kasa sauke kayakin saboda hare-haren da aka koma yi.
Ali al-Za’tari, shugaban hukumar samar da kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, ya ce hare-haren da aka koma yi, sabawa ne ma tabbacin da aka bayar tun farko na tsaron lafiya daga tukkannin bangarorin, ciki har da gwamnatin kasar Rasha.”
An shiga kai hare-haren ne yayin da tawagar ta motocin daukar kaya 13 ta doshi garin Douma don sauke kayankin agajin, wadanda aka kasa kai wat un ranar Litini saboda tabarbarewar yanin tsaro.
Zeid Ra’ad Hussein, babban Kwamishinan MDD kan ‘Yancin dan adam, ya yi kiran da a ladabtar da wadanda su ka aikata rashin Imani a gabashin Ghouta sannan a kuma kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan al’amurorin baya-bayan nan.
Facebook Forum