Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Musulmi Ke Sallar Layya A Duk Fadin Duniya


Mahajjata suna sallah a kewayen Masallacin Namira
Mahajjata suna sallah a kewayen Masallacin Namira

Yau Talata Musulmi a duk fadin duniya ke sallar layya, rana ce ta neman tuba da tsarkakewa

Yau Talata Musulmi a duk fadin duniya suke bikin babar sallah, bayan da Musulmi sama da miliyan biyu ne su ka taru tun jiya Litini don yin hawan Arafa, wanda shi ne cikamakon aikin Haji.

Mahajjata sun yi sahu kafada-da-kafada don ayyukan ibada na wannan muhimmiyar rana ta neman tuba da tsarkaka a inda Musulmi su ka yi imanin cewa Annabi Muhammad (SWA) ya yi hudubarsa ta karshe.

Mahajjata sun ta da kabbara, su na shahada, "La'ila ha ill'Allah" su na "Allahu akbar," ma'ana Allah ne mafifici, a yayin da su ke hawa dutsen Arfa. Musulmi sun yi imanin cewa duk wata addu'ar da aka yi a ranar hawan Arfa ta fi saurin goge zububai da kuma samar da wani sabon masomi mai fa'ida.

Bayan rana ta yi la'asar, sai su ka gangara Muzdalifa don tara duwatsun jifar shaidan, a yau Talata, wacce ita ce ranat ta farko ta sallar layya.

Saudiyya ta ce mahajjata sama da miliyan 2.37, akasari daga kasashen ketare, sun iso don gudanar da ayyukan ibadan na kwanaki biya - wanda aka so duk wani musulmin da ke da hali ya yi akalla sau daya a rayuwarsa.

Masarautar Saudi, mai arzikin man fetur, ta kashe biliyoyin dala wajen tabbatar da tsaron lafiya da kuma dadada rayuwar mahajjata, musamman ma a Mina, inda a baya aka samu hadura mafiya muni da aka taba gani a lokaci irin wannan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG