Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ne Za A Fara Duban Watan Ramadan A Ghana


Wani mutum na dauke da kaji na sayarwa a Ghana a watan Ramadan na 2021
Wani mutum na dauke da kaji na sayarwa a Ghana a watan Ramadan na 2021

Yayin da mafi yawan al’ummar Musulman duniya suka tashi da azumin watan Ramadan a yau Litinin, 11 ga watan Maris, kwamitin Hilal  da aka dorawa alhakin duban wata a Ghana, ta sanar da cewa a yau Litinin din ne za ta fara duban watan Ramadan.

ACCRA, GHANA - A bisa lissafin kwamitin, yau Litinin ne 29 ga watan Sha’aban don haka, a yau ne za a yi duban farko, idan an ga wata sai a fara azumi ranar Talata, idan kuwa ba a gani ba, to wajibi ne a tashi da azumi ranar Laraba.

Hakan ya sa yawancin al’ummar Musulman Ghana ba su tashi da azumi ba yau, domin ba su ji Limamin Limamai na kasa, Dr. Shaikh Usman Nuhu Sharubutu, ya yi sanarwar daukar azumi kamar yadda aka saba ba.

A jawabinsa ga al’ummar Musulmai, Shugaban Kwamitin Hilal na Ghana, Shaikh Alhassan Umar Yussufiyya yace: ‘Kamar yadda fiyayyen halitta ya ce, ku yi azumi da ganin wata kuma ku sha ruwa da ganin wata, domin haka mun nemi watan Sha’aban a ranar 10 ga watan Fabrairu, ba mu ga wata ba, don haka sai muka cika Rajab zuwa kwana 30.

Saboda haka, kidayarmu na kwamitin hilal na kasa, 11 ga watan Maris ne zai zama 29 ga watan Sha’aban. Don haka, kwamitin Hilal, a jagorancin Limamin Limamai na kasa (yau Litinin) za mu duba wata’.

Sai dai Limamin Ahlul Sunnah Wal Jama’a na Ghana, Shaikh Umar Ibrahim, ya sanar ga duk mabiya da su dauki azumi domin an ga wata a kasar Saudiya da wasu kasashen da kuma Ghana.

Ya ce: “Mun ba da labari cewa an ga wata a Saudiya; an gani a Qatar da Kuwait; an gani a Chad, kuma yanzun nan aka kawo mini labarin cewa an gani a Wa, wanda ke nuni da cewa an ga wata a nan Ghana. Don haka, muna sanar da al’umma cewa tashi da azumi yau Litinin wajibi ne, wanda kuma bai tashi da shi ba, to son zuciya ne kawai.”

Game da ganin wata da aka yi a garin Wa dake yankin Sama maso Yamma, Shaikh Yussufiyya ya ce ya kira wanda aka ce ya ga watan, kuma ya tambaye shi lokacin da ya ga watan, sai saurayin ya ce bayan sallar Magariba da ‘dan lokaci.

Yace lallai hakan na nuna rashin ingancin ganin watan, domin ba a ganin ingantaccen wata lokaci mai tsawo bayan Magariba; domin gabanin Magariba ake duban wata, in ji shi.

Wannan sabanin ya sa wasu al’ummar Musulman Ghana sun dauki azumi bisa ga umarnin Limamin Ahlul Sunna wal Jama’a, wasu kuma ba su dauka ba; suka ce sai sun samu umarni daga bakin Limamin Limamai na kasa sannan su dau azumin.

Al’ummar Musulmai kan kwashe tsawon kwanaki 29 ko kuma 30 suna azumi a watan Ramadan da ke da matukar muhimanci domin daya ne daga cikin ginshikan da ke rike da adddinin.

Saurari cikakken rahoto daga Idirs Abdullah:

 Yau Ne Za A Fara Duban Watan Ramadan A Ghana.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG