Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Nijar Ta Ke Cika Shekaru 52 Da Samun 'Yancin Kai


Tambarin Jamhuriyar Nijar

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta aike da sakon fatar alheri ga dukkan al'ummar Nijar tare da jinjina musu.

Yau Jumma'a 3 ga watan Agusta al'ummar Jamhuriyar Nijar suke bukukuwan cikar shekaru 52 da samun 'yancin kai.

Faransa, ta ba kasar ta Nijar cikakken 'yancin kai a ranar 3 ga watan Agustar shekara ta 1960, a bayan da kasar ta zamo mai kwaryakwaryar ikon cin gashin kai karkashin Faransa a watan Disambar 1958, lokacin da aka kafa Jamhuriya ta biyar a Faransa.

A cikin sakon fatar alherin da ta aike ga dukkan al'ummar Nijar kan wannan rana, sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce Amurka tana jinjinawa al'ummar Nijar da kuma gwamnatinsu a saboda kwararan matakan da suka dauka a cikin shekara guda da ta shige domin karfafa cibiyoyin dimokuradiyyarsu tare da wanzar da kwanciyar hankali a yankin Afirka ta Yamma.

Sakatariya Clinton ta ce ta yaba da irin tallafin da Nijar ta ke ba 'yan gudun hijirar da suke gudowa daga rikicin kasar Mali, har ma ga 'yan kasar ta Nijar wadanda suka komo daga Libya a sanadin rikicin da aka yi a can.

Clinton ta ce tsayin dakar da Jamhuriyar Nijar ta yi wajen karfafa dimokuradiyya da kwanciyar hankali tare da karuwar arziki, abin misali ne ga kasashen yankin.

Ta ce Amurka zata ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Jamhuriyar Nijar a zaman kawayen juna wajen kyautata rayuwar dukkan al'ummar Nijar.

XS
SM
MD
LG