Accessibility links

An shiga rana ta bioyu da rufe gwamnatin tarayyara Amurka

Rufe akasarin ayyukan gwamnatin tarayya ta Amurka da aka yi ya sa tilastawa shugaba Barack Obama soke ziyarar biyu daga cikin kasashen Asiya da yake da niyyar rangadi.
A rana ta biyu da fara rufe ayyukan gwamnatin tarayya, fadar White House ta ce Mr. Obama zai soke ziyarar da yayi niyyar kaiwa zuwa malaysia da Philippines, amma ana sa ran zai ziyarci Indonesiya da Brunei, zangonsa na farko a wannan rangadi domin halartar tarurrukan koli na kungiyoyin APEC da Gabashin Asiya.

Daga jiya talata aka fara rufe ayyuka da ofisoshin gwamnatin tarayya a nan Amurka, a bayan da ‘yan majalisar dokoki suka wuce wa’adin da ya kamata su amince da kasafin kudi na tarayya.

‘Yan Republican a majalisar wakilan tarayya su na son su makala batun janye kudin aiwatarwa ko kuma jinkirta fara aiwatar da gagarumin shirin fadada ayyukan kiwon lafiya ga marasa galihu na shugaba Obama ga duk wani kudurin yarda da kasafin kudin gudanar da ayyukan gwamnati.

Dukkan matakan da majalisar wakilan ta dauka na cusa wannan batu cikin kudurin kasafin, majalisar dattijai da ‘yan Democrat suke jagorancinta tana sa kafa tana shurewa domin tilas ita ma ta amince da duk wani kudurin kasafin kudin kafin a mika ga shugaba ya sanya hannu ta zamo doka.

An dakatar da ma’aikatan gwamnatin tarayya su kusan miliyan daya yanzu haka ba tare da albashi ba, yayin da wuraren yawon shakatawa da bude ido ko wuraren tarihi na kasa da ofisoshin gwamnatin tarayya da dama suke rufe.
Wata kuri’ar neman ra’ayoyin jama’a wadda Jami’ar Quinnipiac ta wallafa yau laraba, ta nuna cewa kashi 72 cikin 100 na masu jefa kuri’a a nan Amurka su na yin adawa da rufe ayyukan gwamnatin tarayya da aka yi.
XS
SM
MD
LG