Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Shugaban Amurka Zai Je Bakin Iyakar Kasar Da Mexico


Ziyarar ta shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da aka dakatar da wasu ayyukan gwamnati tsawon kwanaki 19, a yayinda shugaba Trump ke neman kudin gina katanga a bakin iyakar kasar da Mexico.

Bayan da ganawarsu ta baya-baya da shugabannin jam’iyyar Democrat ta kare da ayyana cewa “bata lokaci ne kawai” shi kuma Sanata Chuck Schumer ya kwatanta shugaba Trump a matsayin wanda ba ya iya danne fushinsa, a yau Alhamis shugaban Amurka Donald Trump zai je bakin iyakar Amurka da Mexico.

Ziyarar ta shugaban, zuwa McAllen a jihar Texas, za ta kunshi tarurruka akan tsaron iyaka da kuma zuwa wani ofishin jami’an sintirin iyaka, da kuma yankin iyakar da ke wajen rafin Rio Grande.

Bayannan Jami’an kwastam da na tsaron bakin iyaka sun nuna cewa a yankin kwarin Rio Grande ne cikin ‘yan shekarun nan jami’ai suka fi kama mutanen da suka yi kokarin ketare iyakar zuwa cikin Amurka ba bisa ka’ida ba. A shekarar 2017, bayanai sun nuna cewa a yankin an kama mutane kashi 44 cikin 100 da ke kokarin tsallake iyaka.

Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama a jihar Texas da ke kalubalantar bukatar Trump ta a bashi dala biliyan 5 don gina katanga da kuma manufofin gwamnatinsa akan baki, na shirin yin zanga-zanga yau Alhamis a falin tashar jiragen saman McAllen.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG