Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata 'yan takara ke gangamin neman zabe a Uganda


Gangamin masu goyon bayan shugaban Uganda Yoweri Museveni
Gangamin masu goyon bayan shugaban Uganda Yoweri Museveni

A yau Talata ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisu a kasar Uganda, suke gangamin yakin neman zabensu na karshe.

A ranar Alhamis mai zuwa, al’umar kasar za su garzaya zuwa rumfunan zabe domin zaben shugaba Yuweri Museveni wanda ke neman shugabancin kasar a wa’adi na biyar, ko kuma dan takarar ‘yan adawa, wanda hakan ka iya basu damar samunn sabon shugaban kasa tun shekarar 1986.

Museveni ya karbi shugabancin kasar, bayan da ya yi juyin mulki, ya kuma lashe zabukan da aka yi a shekarun 2006 da 2011, zabukan da masu lura da al’amura suka ce an tafka magudi tare da yin barazana ga ‘yan adawa.

A jiya Litinin, ‘yan sanda kasar ta Uganda suka tsare abokin hamayyar Museveni, Kizza Besigye na dan wani lokaci, yayin da ya ke yakin neman zaben sa a babban birnin kasar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, ‘yan sanda sun yi amfani da

Barkonon tsohuwa akan wadanda suka halarci gangamin siyasar.

Rahotanni sun ce gabanin a sako shi, an kai shi wani wuri da ke wajen birnin Kampala.

Shugaban ‘yan sanda kasar, ya zargi Besigye da keta wasu ka’iodjin yin kamfe.

XS
SM
MD
LG