Kafin ‘yan Majalisar Dokokin Amurka su taru a yau Talata domin sauraren jawabin halin da kasa ke ciki na shekara-shekara, wanda Shugaba Donald Trump zai gabatar a karo na uku, za a ba Sanatoci dama su yi na su jawaban a gaban zauren majalisar.
Jawaban na su, za su karkata kan bayyana matsayarsu dangane da shari’ar neman tsige Shugaban.
Jawaban sanatocin wadanda suke a matsayin masu taimakawa alkali wajen yanke hukunci a wannan shari’a, ba sa cikin bangaren sauraren karar ta neman a tsige Trump.
Ana kyautata zaton cewa, zai yi wuya su sauya matsayarsu, inda ga dukkan alamu, ake tunanin za su wanke Trump daga zargin, idan sun zo kada kuri’a a gobe Laraba.
A jiya Litinin, bangaren ‘yan Democrat da suka shigar da karar neman a tsige Trump da kuma lauyoyin da suke kare shugaban, suka yi jawaban kammala muhawarorinsu, bayan da aka kwashe mako biyu ana sauraren bahasinsu.
Facebook Forum