Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za A Tabka Wani Irin Sanyi Mai Tsanani A Amurka

Yadda yanayi ya ke kenan a sassan New Jersey na Amurka
Yadda yanayi ya ke kenan a sassan New Jersey na Amurka

Yau Jumma’a za a yi wani irin sanyin da ba a taba yi ba, wanda zai yadu a fadin yankin tsakiyar yammacin Amurka da kuma yankin gabar gabashin kasar, kwana guda kawai bayan da wata mummunar guguwa mai baza dusar kankara, wadda ta jibga dusar kankara da iska mai tsanani da ambaliyar kankara duk a yankin tekun Atilantika.

Yanayi mai cike da iska mai tsananin sanyi zai addabi wasu manyan biranen Amurka wajen 25 inda ake kyautata zaton za a tabka sanyin kasa da 40 a ma’aunin Celsius a yau Jumma’ar – wanda hakan ba kawai yanayi ne mara dadi ba, mai hadarin gaske ne.

Masu tunanin samun taimako a Florida za su sha mamaki. Da kayar ma ma’aunin ‘tamomita’ ya kai Celsius 10 a biranen da ma aka sansu da zafi kamar su Tampa da Orlando.

An gargadi miliyoyin mutane kan mummunar iska mai baza dusar kankara. An rufe makarantu da ofisoshi, an soke dubabban tafiye-tafiyen jiragen sama kuma tuni masu ayyukan ceto ke ta fadi-tashin ceto wasu mutane da su ka makale. Dubban gidaje basu da wutar lantarki.

Zuwa yanzu an samu mace-mace masu nasaba da wannan matsala har 14.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG