Accessibility links

Yau Za A Yi Jana'izar Yarima Nayef Bin Abdul-Aziz al-Saud


Marigayi Yarima Nayef bin Abdul-Aziz al-Saud

Yayin da ake hasashen cewa Yarima Salman, ministan tsaro kuma kanin Sarki Abdullahi, shi zai zamo sabon Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Sa'udiyya

Yau lahadi za a yi jana’izar marigayi Nayef bin Abdul-Aziz al-Saud, Yarima mai jiran gado na kasar Sa’udiyya wanda ya rasu jiya asabar yana da shekaru saba’in da wani abu da haihuwa.

Wata sanarwar da kafofin yada labaran Sa’udiyya suka bayar ta ce Yarima Nayef ya rasu a wajen Sa’udiyya. Kafofin labarai suka ce ya rasu ne a birnin Geneva ta kasar Switzerland, inda ya je jinyar wani rashin lafiyar da ba a bayyana ba. Fadar sarkin Sa’udiyya ta ce za a yi jana’izarsa yau lahadi a Makka.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya mika sakon ta’aziyya ga Sarki Abdullahi da gidan sarauta da kuma al’ummar Sa’udiyya. Wata sanarwar fadar White House ta ce an kulla kawance mai karfi da nagarta wanda ya ceci rayukan mutane masu yawa ‘yan Sa’udiyya da Amurka wajen yaki da ta’addanci karkashin jagorancin Yarima Nayef.

Shi dai Yarima Nayef, tsohon ministan harkokin cikin gidan Sa’udiyya, ya zamo Yarima mai jiran gado a watan Oktoba, bayan rasuwar mai rike da wannan mukami Yarima Sultan bin Abdul-Aziz al-Saud. Mutumin da ake kyautata zaton zai gaji wannan kujera a yanzu shi ne Yarima Salman mai shekaru 76 da haihuwa, kanin Sarki Abdullahi, kuma mutumin da aka nada ministan tsaro a watan nuwamba bayan da ya shafe shekaru fiye da 40 yana gwamnan Riyadh.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG