Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Masu Tserewa Daga Libya Yana Karuwa


Zaratan sojoji na wani birged dake karkashin jagorancin dan autan shugaba Gaddafi, Khamis, a lokacin da suka isa wani wuri mai nisan kilomita 10 a gabas da Zawiya, litinin 28 Fabrairu, 2011.

Yayin da sojoji masu goyon bayan shugaba Muammar Gaddafi da masu adawa da shi suke ci gaba da yin ba-ta-kashi

Yawan mutanen dake tserewa daga Libya yana karuwa, yayin da aka kasa ganin wata alamar saukin fadan da ake gwabzawa na neman mallakin wannan kasa dake Afirka ta Arewa. An yi kiyasin cewa a yanzu, mutane fiye da dubu 110 ne, akasari baki ‘yan kasashen waje, suka tsere zuwa Masar a gabas, ko kuma Tunisiya a yamma.

Amma a jiya litinin, babban jami’in kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, yace da yawa daga cikin wadanda ke son barin kasar sun kasa yin haka a saboda ba su da sukunin tserewa.

Masu fashin baki kan al’amuran Gabas ta Tsakiya sun yi hasashen cewa za a jima ana gwagwarmayar neman mallakar Libya, inda masu goyon baya da masu yin adawa da Muammar Gaddafi zasu ci gaba da karfafa matsayinsu. Suka ce tana yiwuwa kasar Libya ta fada cikin yakin basasa.

Muammar Gaddafi ya fadawa ‘yan jarida jiya litinin cewa mutanen Libya su na sonsa, kuma a shirye suke su sadaukar da rayukansu a kansa. Ya fadi wannan magana a Tripoli, babban birnin kasar, kuma birni mafi girma da ya rage a hannun dakarunsa. Haka kuma ya sake yin watsi da duk wani tunanin cewa zai yi murabus.

A halin da ake ciki, an yi wata zanga-zangar ta nuna kin jinin gwamnatin Gaddafi jiya litinin. Dakarun tsaro sun tarwatsa wasu daruruwan mutane da suka taru domin zanga-zanga a unguwar Tajouri ta Tripoli su na rera baitocin nuna kin jinin Gaddafi.

A Misurata, kimanin kilomita 200 a gabas da Tripoli, shaidu sun ce an ba hammata iska a tsakanin dakarun ‘yan tawaye da masu yin biyayya ga Gaddafi. An ce mazauna Misurata da birnin Zawiya mai matatar mai a yammacin kasar, su na jan damarar fuskantar farmakin da ake tsammanin sojojin Gaddafi zasu kai domin kwato garuruwan.

XS
SM
MD
LG