Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaya za'a magance matsalolin da ambaliyar ruwa ke haifarwa?


Hotun ambaliyar
Hotun ambaliyar

Mutane da dama sun yiwa wakilin sashen Hausa Nasiru El Hikaya bayanin halin da suka shiga na ban tausayi, a sakamakon ambaliyar ruwa a garin Suleja dake kusa da Abuja babban birnin taraiyar Nigeria inda aka samu hasarar rayuka.

Mutane da dama sun yiwa wakilin sashen Hausa Nasiru El Hikaya bayanin halin da suka shiga na ban tausayi, a sakamakon ambaliyar ruwa a garin Suleja dake kusa da Abuja babban birnin taraiyar Nigeria inda aka samu hasarar rayuka.

Bana an yi ta samun ruwan sama kamar da bakin kwarya, kafin mutane su ankara sai sun tsinci kansu a tsakiyar ruwa. Kwanan nan ma a wani wuri dab da garin Wurodole dake kan iyakar Gombe da Bauchi arewa maso gabashin Nigeria, wata ambaliyar ruwa ta keto gonaki ta rastsa kan titi harma ta yanke zirga zirgan motoci na tsawon sa’a hudu, wadanda kuma suka yi kasadar tsalakawa, ruwa ya yi kusan awon gaba da su.

Wani kwarare akan tsara birane dake Abuja, Injiniya Mohammed Bello, ya yiwa wakilin sashen Hausa Nasiru El Hikaya bayanin babban dalilin dake haddasa ambaliyar ruwa. Yace ya kamata mutane su san muhimmancin bude magudanan ruwa da kuma gyara su idan lokaci yayi,da kuma rashin yin gine gine akan magudanan ruwa.

A gefen gwamnati kuma, Injiniya Mohammed Bello yace ya kamata a duk lokacin da aka fadada wuraren gina gidaje, ya kasance an tanadi magudanan ruwa da hanya wadatacciya. Sa’anan kuma a rika dubawa akai akai, ko lokaci lokaci ana sa ido aga abinda za’a yi, kuma ayi shi cikin lokaci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG