Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yellen ta Zama Mace ta Farko da Zata Shugabanci Babban Bankin Amurka


Janet Yellen sabuwar shugabar Babban Bankin Amurka
Janet Yellen sabuwar shugabar Babban Bankin Amurka

A tarihin Amurka mace bata taba zama shugabar Babban Bankin kasar ba sai a wannan karon

Majalisar dattijan Amurka ta amince da nadin Janet Yellen, a matsayin sabuwar shugabar babban Bankin Amurka. Da wannan nadin, Madam Yellen ta shiga sahun manya masu tasiri a fagen tattalin arziki a duniya.

A kuri’ar amincewa da zabenta senatoci 56 ne suka amince wakilai 26 suka kada kuri’ar kin amincewa. Kuri’a 51 kawai ake bukata domin mutum ya sami amincewa.

Shugaba Barack Obama yace Amurkawa sun sami jaruma wacce ta fahimci burin manufofin tattalin arziki shine inganta rayuwa da ayyukan ma’aikata da iyalansu.

Yellen zata kasance mace ta farko da zata shugabanci babban bankin Amurka cikin shekaru dari da kafuwarsa. Zata maye gurbin shugaban bankin na yanzu Ben Bernanke wanda wa’adin aikinsa zai kare a karshen watan nan.
XS
SM
MD
LG