Wani harin roka da aka kai a bikin yaye mayakan ‘yan awaren kudancin Yemen yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 10, ya kuma raunata wasu gwammai.
Wani mai magana da yawun mayakan da ke hadin gwiwa da Saudi Arebia ya zargi mayakan Houthi da ke da goyon bayan Iran a Yemen da hannu a kai harin.
Wadanda suka tsira sun taimakawa wadanda suka raunata daga harin na roka, a kusa da wata rumfar ‘yan kallo a wajen bikin yaye dakarun mayakan ‘yan awaren.
Wani hoton bidiyo ya nuna fashewar rokar sa’adda ta daki rumfar ‘yan kallon.
Irin wannan harin da mayakan na Houthi suka kai a watan Agusta, ya kashe babban kwamandan mayakan, Janar Munir Mahmoud Mashali.
Majed Al Shouaiby, shine mai magana da yawun dakarun tsaro ya shaidawa kafar yada labaran larabawa cewa, ‘yan Houthi sun harba roka a kan faretin dakarun daga bangaren Arewacin garin Dhalea, inda aka kai harin.
Sai dai kawo yanzu mayakan na Houthi basu dauki alhakin kai wannan harin ba.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 17, 2021
Wani Ayarin Baki Masu Kaura Na Dosar Amurka Daga Honduras
-
Janairu 16, 2021
India Ta Kaddamar Da Shirin Bada Riga Kafin COVID-19
-
Janairu 11, 2021
WHO Za Ta Aika Wata Tawagar Bincike China
-
Janairu 06, 2021
An Kama ‘Yan Gwagwarmayar Rajin Dimokradiyya Sama da 50 a Hong Kong
Facebook Forum