Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Yunkurin Juyin Mulki A Mali Bai Sami Nasara Ba.


Sojojin Mali.

Rahotanni daga kasar Mali sun ce sojojin da suka hambarar da shugaban kasar da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a watan Maris sun samu nasarar murkushe wani yunkurin da aka yi na yi musu juyin mulki su ma.

Rahotanni daga kasar Mali sun ce sojojin da suka hambarar da shugaban kasar da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya a watan Maris sun samu nasarar murkushe wani yunkurin da aka yi na yi musu juyin mulki su ma.

Tun ranar litinin sojoji masu tsaron lafiyar hambararren shugaba Amadou Toumani Toure, suka gwabza da bijirarrun sojojin da suka yi juyin mulki a Bamako, babban birnin kasar, a wani yunkurin kawar da su daga kan mulki. Madugun juyin mulki Kyaftin Amadou Sanogo, ya fada cikin wani jawabin da yayi ta telebijin cewa dakarunsa ne suke rike da muhimman cibiyoyin birnin har yanzu.

Wani kakakin gwamnatin rikon kwarya da aka kafa a bayan juyin mulkin, Hamadoun Toure, yayi kira ga al’ummar Mali da su kwantar da hankulansu abayan wannan fada da ya kashe mutane akalla 15.

Jiya talata jami’an gwamnatin mulkin soja sun ce dakaru masu biyayya ga tsohon shugaban kasar sun tsere. Shi ma ofishin jakadancin Amurka dake Bamako yace da alamun yunkurin sojojin hambararren shugaban na sake kwato mulki ya ci tura.

Bijirarrun sojojin da suka kwaci mulki sun zargi Mr. Toure da laifin kasa samar da kayan fadan da ya kamata ga sojojin kasar domin takalar tawayen da Abzinawa suke yi a arewa.

XS
SM
MD
LG