Accessibility links

Yunwa da Rashin Aiki su ne Sanadiyar Tabarbarewar Tsaro a Arewacin Najeriya


Sojojin tsaro a jihar Kaduna

Shugaban kungiyar dattawan arewa ya ce yunwa da rashin aikin yi ne musabbabin haddasa tabarbarewar tsarin tsaro a arewacin Najeriya

Shugaban Kungiyar dattawan arewa Farfasa Ango Abdullahi ya ce yunwa da rashin aikin yi su ne umalubaisan tabarbarewar tsarin tsaro a rewacin Najeriya.

Farfasa Ango Abdullahi wanda yake jawabi a wurin taron bunkasa lardin Zazzau ya ce idan ana son a samu zaman lafiya to wajibi ne a binciki tushen lamarin. Ya ce abubuwan da suka fi damuwarsa ba aika-aikar Boko Haram ba ne ko kashe-kashe da a keyi a jihohin Filato ko Binuwai domin duk wadannan tashin hankali ne, amma rashin kwanciyar hankali suka fi damunsa. Ya ce akwai banbanci tsakanin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali.

Kahse-kashe a Filato ko Binuwai ko kuma wani lokacin a jihar Kaduna babu shakka tashin hankali ne. Amma abun da ya fi damun mutane shi ne idan maigida ya tashi da safe ya gama sallar asubahi zai shiga tunanin ko akwai koko da kosai da iyalinsa zasu yi karin kumallo da su? Idan har babu to maigida ya shiga rashin kwanciyar hankali. Idan har dimbin jama'a suna cikin irin wannan hali na rashin ci da sha to kada a yi tsammanin ba za'a samu tashin hankali ba. Irin wannan rashin kwanciyar hankali shi ne yake haifar tashin hankali. Ya ce ba yawan sojojin da suka hana su sukuni ba ne tsaro ko fafitikar da sojoji ke yi da 'yan ta'ada da suka kasa ci amma kamata ya yi a duba ina makasudan wadanda suka kawo halin da a ke ciki su ke.

Shi kuma shugaban kungiyar hada kawunan al'umomin 'yan kudancin Kaduna Dr. Ephraim Goje jaddada hadin kan 'yan Kaduna ya yi. Idan zagezagi da 'yan kudancin Kaduna sun hada kai zasu iya habaka jihar Kaduna fiye da yadda ya kamata. Misali idan an yi makaranta a Zaria za'a samu 'yan kudancin Kaduna a cikinta haka ma idan an gina makaranta a kudancin.

Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati Alhaji Yahaya Aminu wanda ya wakilci gwamnan jihar Alhaji Mukhtari Ramalan ya yi murnar irin dakwon zumunci dake tsakanin kungiyoyin biyu. Ya ce gashi shugaban kungiyar hadin kawunan 'yan kudancin Kaduna sukapo Dr. Goje ya yi jawabi, ya bada shawarwari har ma ya bada gudunmawa. Ya ce idan aka wayi gari a ka ce manufofin kungiyar 'yan zazzau da na 'yan kudancin Kaduna sun zama daya to za'a samu zaman lafiya da cigaba. Mai girma gwamna yana kiran al'ummomin jihar su yi tafiya tare irin wannan domin samun cigaba.

Ita kungiyar zazzau tana fafitikan tabbatar da tsaro da samun ilimi da aikin yi.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara.
XS
SM
MD
LG