Accessibility links

Za a Bincike Masababin Mutuwar 'yan Kasar Ghana Da Aka Kashe Makon Jiya


'Yan Kasar Ghana Suna Hakar Zinari
Kasashen Ghana da Ivory Coast ko Cote D’Ivoire, zasu kaddamar da wani kwamitin binciken hadin guiwa domin bin diddigin mutuwar ‘yan kasar Ghana su 8 da aka kashe makon jiya lokacin wasu hare-haren tsallaken iyaka da aka kai kan wasu cibiyoyin sojan kasar Ivory Coast.

Nan da nan hukumomin IC suka dora laifin hare-haren a kan ‘yan gudun hijira magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo wanda aka gurfanar gaban shari’a ana tuhumarsa da aikata laifuffukan cin zarafin bil Adama.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Ghana, Chris Kpodo, ya fadawa Muryar Amurka cewa gwamnatin Ghana ba zata kyale kasar ta zamo sansanin ayyukan ‘yan gudun hijiran IC dake kokarin yin zagon kasa ma kasarsu ba.

IC ta rufe bakin iyakokinta da Ghana makwabciyarta a bayan hare-haren da aka kai a kan wani garin dake bakin iyaka da kuma Abidjan, cibiyar kasuwancin kasar.
Ba a bayyana lokacin gudanar da wannan aikin bincike ba.
XS
SM
MD
LG