Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Fara Bincike Akan Katsalandar Rasha a Zaben Amurka na Shekarar 2016


Ranar 20 ga watan nan na Maris ne za a fara gudanara da bincike akan Katsalandar da Amurka ke zargin Rasha tayi a zaben da ya gabata.

Kwamitin dake kula da ayyukan tattara bayanan sirri na majalisun dokokin Amurka zai gudanar da binciki kan katsalandar da Rasha ta yi a zaben Amurka a bainar jama’a ranar 20 ga watan nan na Maris, inji shugaban kwamitin a majalisar wakilai, Devin Nunes a jiya Talata.

A cikin wadanda za su bayyana gaban kwamitin don ba da bayani, akwai darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI James Comey da ya kasance a tsakiyar wannan batu saboda kane-kanen da ya yi a binciken sakwannin Email din Hillary Clinton, sai kuma Mike Rogers darektan hukumar tsaro da kuma John Bernnan tsohon shugaban ma’aikatar leken asirin Amurka ta CIA.
Mr. Nunes ya fadawa manema labarai cewar saboda muhimmancin wannan batu, zai yi iya bakin kokarinsa ya ga cewa an saurari bahasin a baina jama’a.

Shugaba Donald Trump dan kansa ya kara zafafa wannan batun a kan binciken katsalandar da Rasha ta yi a zaben kasar a karshen makon jiya, inda ya rubuta a kan shafinsa na tweeta cewa tsohon shugaba Barack Obama ya sa an yi masa kutse a wayoyin gidansa na New York, zargin da kakakin Obama ya karyata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG