Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Bude Filayen Jiragen Sama A Najeriya


Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika
Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika

Za a bude tashoshin jiragen sama na biranen Abuja da Legas a ranar takwas ga watan Yuli domin zirga-zirgar jiragen cikin gida a cewar ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika.

Ministan ya kuma bayyana cewa, za a bude filayen jiragen sama na Kano da na Fatakwal da Owerri da kuma Maiduguri a ranar 11 ga watan Yuli.

Sauran filayen jirage a kasar kuma za a bude su ranar 15 ga watan Yuli.

A cikin sanarwar da ya kafa a shafinsa na twitter (@hadisirika), Hadi Sirika ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a bayyana ranar da jirage zasu fara fita da kuma shiga Najeriya.

Filayen jiragen dai sun kasance a garkame na tsawon watanni sakamakon kokarin takaita yaduwar cutar Coronavirus wacce ta addabi duniya gabadaya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG