A gobe Lahadi za’a fafata wasar karshe ta gasar zakarun Turai tsakanin Bayern Munich ta kasar Jamus da PSG ta kasar Faransa, a birnin Lisbon.
Wannan ne karo na 11 da Bayern din za ta fafata wasar karshe ta gasar da ta taba lashewa sau 5 a can baya, yayin da ita kuma PSG za ta buga wasan karshe ta gasar karo na farko a tarihi.
Bayan ragargaza Barcelona da ci 8-2 a wasan QF, Bayern Munich ta kuma doke Lyon da ci 3-0 a wasan kusa da na karshe, a yayin da ita ma PSG ta yi nasarar doke Leipzig da ci 3-0, wanda ya ba ta damar kai wa a wasar karshe ta gasar.
Facebook Forum