Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Fara Allurar Rigakafin Moderna A Najerya - NPHCDA


Jamian Najeriya sun karbi rukunin farko na rigakafin corona a Abuja.
Jamian Najeriya sun karbi rukunin farko na rigakafin corona a Abuja.

Hukumar kula da lafiya matakin farko ta Najeriya PHCDA tace za’a fara aikin gudanar da rigakafin annobar cutar korona nau’in moderna da gwamnatin Amurka ta baiwa Najeriya.

Shugaban hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya Dr. Faisal Shu’aibu ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa za’a fara aikin gudanar da allurar a ranar litinin 16 ga watan da muke ciki.

Tunda farko dai an shirya fara rigakafin ne a yau Talata 10 ga watan Agusta, to amma sai aka dage domin baiwa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC da sauran hukumomin lafiya damar gudanar da bincike da duk wani tsare-tsaren da ya dace domin tabbatar da ingancin allurar.

Jadawalin adadin rigakafin Korona birus da aka bayar a Najeriya.
Jadawalin adadin rigakafin Korona birus da aka bayar a Najeriya.

Da take gabatar da jawabi a wajen taron manema labaran, shugabar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce a halin da ake ciki yanzu hukumar ta gama gudanar da duk wani bincike da ya dace game da allurar rigakafin ta moderna ta kuma tabbatar da ingancin ta.

Shugabann hukumar ya kuma bayyana cewa a yau talata Najeriya zata karbi allurar J&J kimanin dubu dari da saba’in da shida (176,000) da za’a yiwa mutanen da ke zaune a yankunan da ke da wahalar zuwa, duba da cewa idan aka yi sau daya ya wadatar, sabanin sauran alluran da ake yi sau biyu.

Dr. faisal ya kuma kara da cewa kasar zata karbi alluran AstraZanneca dubu dari bakwai (700,000) don gudanar dasu ga wadanda suka karbi kashi na farko.

Shima a nasa bangaren ministan lafiya na Najeriya Dr. Osagie Ehanire ya yabawa sauran hukumomin lafiya da da sauran masu ruwa da tsaki game da irin aikin da suke gudanarwa don yaki da annobar korona da sauran cutuka masu yaduwa.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan da kwamitin da Shugaban kasa Najeriya Muhammadu ya kafa don yaki da annobar cutar korona ya fitar da sanarwa ta hannun daraktan yada labarai na kwamitin Mista Willie Bassey cewa an dage fara aikin gudanar da rigakafin.

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG