Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Fara Hana Amurkawa Bulaguro Zuwa Koriya Ta Arewa


An kafa dokar hana Amurkawa bulaguro zuwa kasar Koriya ta Arewa, domin kare su daga fadawa hannu da dauresu ba tare da sun aikata laifi ba.

Amurka tace daga ranar daya ga watan satumbar wannan shekara zata fara hana ‘yan kasarta zuwa Koriya ta Arewa.

Bayanin da aka bayar a kundin bayanai na gwamnatin Tarayyar Amurka din ya nuna cewa an dauki matakin ne don kare Amurkawa daga kasadar a kama su kuma ayi musu tsarewa ta dogon lokaci.

A halin yanzu kuma, manyan jami’an diplomasiyyar Amurka sun sanarda shugabannin kasar ta Koriya ta Arewa cewa “Amurka ba makiyarsu ba ce.” Amurka na wannan bayanin ne duk da cewa bata janye komi ba cikin jerin matakai da zata iya dauka na takawa shirin makamai masu linzami da na Nukiliya da kasar take yi burki.

A taro da manema labarai da yayi, Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yace "Amurka bata neman canjin gwamnati a koriya ta Arewa, bata bukatar ganin rugujewar gwamnatin, bata ma neman a gaggauta hadewar kasashen cikin gaggawa ba, sannan kuma Amurka ba wai tana neman wata hujja na tura sojojinta cikin kasar ta KTA ba."

Tillerson yace duk da take-taken tsokana da KTA ke dauka kan Amurka, Tilerson yace Amurka na fatar watan wata-rana kasashen biyu zasu zauna su tattauna hanyoyin samun masalaha a cece-kuccen nasu

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG