Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Fara Wasannin NBA Kafin Karshen Shekarar 2020

A karshen mako hukumar wasannin Kwando ta NBA ta tabbatar da cewa za ta soma wasanni kafin karshen shekara. Hukumar ta ce wasannin zasu fara ne daga ranar 22 ga watan Disamba.

An dai dade ana dakon wannan labarin, ana kuma sa ran ‘yan wasa zasu kafa sansanin horarwa daga ranar daya ga watan Disamba, makoanni kalilan kafin soma wasannin.

Duel Nikole Jokića i Lebrona Džejmsa u trećoj četvrtini pete utakmice finala Zapadne konferencije (Foto: Reuters/Kim Klement-USA TODAY Sports)
Duel Nikole Jokića i Lebrona Džejmsa u trećoj četvrtini pete utakmice finala Zapadne konferencije (Foto: Reuters/Kim Klement-USA TODAY Sports)

Annobar COVID-19 da tayi sanadiyar dakatar da kakar wasan shekarar 2019 da 2020, mutanen da dama ne ke tambaya ko shin ya wannan annobar zata shafi wasannin nan gaba. Kungiyar NBA bata iya kammala daukar shawarwarinta ba har sai 11 ga watan Oktoba, lamarin da ya hanata soma wasanni a tsakiyar oktoba kamar yanda ta saba.

Los Angeles Lakers' LeBron James (23) and Anthony Davis (3) celebrate after the Lakers defeated the Miami Heat 103-88 in Game 6 of basketball's NBA Finals Sunday, Oct. 11, 2020, in Lake Buena Vista, Fla. (AP Photo/Mark J. Terrill)

Wani batu da ke tunani akai kuma shine, NBA zata saurara har sai an fito da maganin rigakafin corona din kafin ta bada ‘yan kallon damar sake shiga wuraren wasan da yawa. Wasu filayen wasa sun ba ‘yan kallo dama shiga amma kasa da adadin da suke dauka.

Amma koma baya da wannan matakin zai huskanci shine ba a san lokacin da maganin zai fito ba.

Facebook Forum

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG