Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gurfanar Da Tsohon Shugaban Gambiya Yahya Jammeh Bisa Zarginsa Da Kisa


Yahya Jammeh da matarsa Zineb Jammeh
Yahya Jammeh da matarsa Zineb Jammeh

Wannan na daga cikin shawarar da hukumar da aka dorawa alhakin bincike da sasantawa tareda biyan diyya TRRC atakaice ta bayar na bukatar da a gurfanar da tsohon shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh.

Sun bukaci da a gurfanar da tsohon shugaban kasar ne tare da wasu mutane su goma sha uku bisa laifukan da suka hada da kisa da azabtarwa, da cin zarafi, tare da tilatsa bacewar bakin hauren da adadinsu ya kai 67 duk ya’yan Afrika ta Yamma.

Sai dai ba wannan kadai bane, hukumar ta TRRC ta bukaci gwamnatin Gambia ta samarwa al’ummar da wannan al'amarin ya shafa, diyyan 612,000 na dalolin Amurka, a cewar wani mista Martin Kyere, daya daga cikin bakin hauren da suka kubuta daga hannun dakarun tsohon shugaban Gambiyan.

Wani jirgi dauke da 'yan gudun hijira a Girka
Wani jirgi dauke da 'yan gudun hijira a Girka

A ranar 22 ga watan Yulin 2005 ne dakarun tsaron Gambiya suka cafke bakin haure da aka ce su duka ya’yan Afrika ta Yamma ne bisa zarginsu da yunkurin kifar da gwamnatin Yahya Jammeh a daidai lokacin da kwalekwale mai inji da ke dauke dasu ya tsaya a Gambiya, suna kan hanyar tsallake tekun meditereniya zuwa nahiyar Turai.

A cikin kwana 10 aka kashe bakin hauren da suka hada da ‘yan Ghana 44, da ‘yan Nigeria guda 9, da ‘yan Togo su 2 tare da wasu mutanen Cote Divoire da Senegal da kuma wani ‘dan Gambiya, dab da iyakar Senegal da Gambiya sannan aka saka gawarwakinsu acikin wata rijiya.

Wasu 'yan kasar Libiya suna kauracewa kasar ta tekun Baharum
Wasu 'yan kasar Libiya suna kauracewa kasar ta tekun Baharum

Yayin wani taro da manema labaru a birnin Kumasi a jihar Ashantin kasar Ghana Mista William Nyarko shugaban kungiyar JUSTICE2JAMMEH da ta tsaya tsayin daka domin kwato hakkin al’ummar da akaci zarafinsu ya jinjinawa kwamitin tare da bukatar da gwamnatin Adama Barrow na Gambiya da ta sake duban kudin diyyan saboda yayi kadan.

Sai dai kuma hukumar TRRC ta bukaci a kafa kwamitin binciken kasa da kasa domin gano hakikanin wurinda gawarwakin suke don afito dasu..

Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam:

Za'a Gurfanar Da Tsohon Shugaban Gambiya Yahya Jammeh Bisa Zarginsa Da Kisa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00


XS
SM
MD
LG