Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutum Hudu A Babban Birnin Somaliya


Wani harin kunar bakin wake da aka kai a Somaliya
Wani harin kunar bakin wake da aka kai a Somaliya

Akalla mutum hudu ne suka mutu, sannan wasu fiye da 10 kuma suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wani shagon shan shayi da ke wajen wata cibiyar horar da sojoji a gundumar Wadajir ta Mogadishu, a cewar ‘yan sanda.

‘Yan sandan sun ce dan kunar bakin waken ya shiga dakin shan shayin, ya noke kamar abokin cinikaya, ya zauna yana shan shayi. Bayan dan wani lokaci kadan sai bam din ya tashi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Manjo Abdifatah Aden, ya ce da gangan dan kunar bakin waken ya auka wa abokan cinikin da suke shan shayi. Aden ya ce mutane 14 ne suka jikkata sakamakon fashewar, wasu hudu daga cikinsu sun mutu bayan an kwashe su daga wurin.

Nan take kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin harin na ranar Talata.

Hotunan da aka dauka daga wurin da lamarin ya faru sun nuna dakin shayin ya lalace sosai sakamakon fashewar.

'Yan sanda sun ba da rahoton wani fashewa na biyu a wannan gundumar kimanin sa'o'i 2 bayan fashewar farkon. Fashewar bam din na biyu ya fito ne daga na'urar da ke makale da wata motar wani kamfani mai zaman kanta amma ba a samu asarar rai ba a cewar 'yan sanda.

Irin wannan fashewar bam wanda ake iya hadda shi daga gida, ya raunata wakilin gwamnatin Somaliya kuma tsohon dan jarida Mohamed Ibrahim Moalimuu a ranar Lahadin da ta gabata bayan wani dan kunar bakin wake ya ruga da gudu zuwa motarsa tare da tayar da wata rigar bamabamai.

Moalimuu ya samu raunuka a hannunsa da kafarsa. Tuni dai aka dauke shi zuwa Turkiyya domin jinya.

XS
SM
MD
LG