Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za’a Sake Bude Makarantu A Jihar Katsina


Gwamnan jihar Katsaina, Aminu Bello Masari (Twitter/@GovernorMasari)
Gwamnan jihar Katsaina, Aminu Bello Masari (Twitter/@GovernorMasari)

Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar 4 ga Oktoban shekarar nan ta 2021 a matsayin ranar da za ta sake bude makarantu gwamnati da na masu zaman kan su.

Kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar Katsina Malam Sani Danjuma ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan ilimin jihar a ranar Lahadi.

Haka kuma sanarwar ta ruwaito kwamishinan Ilimin jihar, Dakta Badamasi Lawal, yana cewa za'a koma aikin koyar da darussa a ranar Litinin 4 ga Oktoba ga dukannin daliban jihar har da na makarantun kwana-kwana.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), tun da farko an tsara cewa makarantu za su ci gaba da aiki a ranar 13 ga watan Satumba, amma an jinkirta don ba da damar daidaita manhajar lokacin makarantun.

Idan ana iya tunawa, a baya-bayan nan aka yi ta yada jita-jitar cewa an saka ranar 13 ga watan Satumba a matsayin ranar komawa makarantu, saidai an dage ranar don bada damar yin gyara a jadawalin koyarwa na makarantun jihar ta Katsina, kamar yadda kamafanin dillancin labaran Najeriya wato NAN ya ruwaito kwamishinan ilimin jihar na cewa.

Kwamishinan ilimin jihar dai ya kuma ce an tsaida ranar sake bude makarantun ne don kammala ayyukan zangon karatu na 3 na shekarar 2020-2021 kuma ba’a bar makarantun a yankunan da ke fuskantar kalubalen tsaro a baya ba a cikin lamarin.

Lawal ya kuma yi kira ga dukkan makarantu a duk fadin jihar da su kiyaye tsauraran matakan kariya daga cutar korona birus, musamman amfani da man tsabtace hannu, amfani da takunkumin rufe fuska da kiyaye ba da tazara tsakanin jama’a.

Kazalika, kwamishinan ya kuma kara tabbatar wa iyaye da daliban makarantun jihar da daukan isassun matakan tsaro, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da kare rayukan su.

Lawal ya kuma yi kira ga iyaye da sauran jama’a da su ci gaba da addu’a don kawo karshen matsalolin tsaro a jihar, da sauran jihohin Arewacin Najeriya.

Jihar Katsina dai ta yi ta fama da hare-haren yan bindiga wadanda suka kunno da salon sace yaran makarantun gwamnati daga ranar 11 ga watan Dismabar shekarar 2020 ciki har da yaran makarantar sakandaren kimiya da ke Kankara, inda su ka yi awon gaba da dailabai akalla 344.

Sauran jihohin Arewa maso yamma kamar su Kaduna Zamfara Katsina Sakkwato da Neja ma sun sha fama da hare-haren yan bindiga a shekarun baya-bayan nan.

Mukarabban gwamnatoci a matakin jihohi da tarayya sun ce suna ci gaba da daukar kwararran matakai don kawo karshen matsalolin tsaro a Najeriya.

XS
SM
MD
LG