Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Soma Shirin Sulhu Da Taliban A Afghanistan


Dakarun wanzar da zama lafiya a Afghanistan
Dakarun wanzar da zama lafiya a Afghanistan

Shirye-shirye sun kankama na soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Afghanistan da 'yan Taliban, domin kai karshen yaki a karkashin jagorancin Amurka.

Bangarorin da ke fada da juna a Afghanistan sun shirya soma tattaunawar samar da zama lafiya ta farko a farkon mako mai zuwa a Qatar, a yayin da Amurka ke ta yin kira gare su da su yi amfani da wannan dama mai cike da tarihi domin kai karshen yaki da ya dauki tsawon lokaci a kasar.

Sasantawar da Amurka ta jagoranta da aka kira ta sulhu na cikin gida na Afghanistan, za ta hada hancin wakilan gwamnatin Afghanistan na Doha da na mayakan Taliban, wadda take da ofishinta a babban birnin kasar da ke gabar teku.

A ranar Assabar Taliban ta ba da sanarwar tawagarta ta sulhun mai wakilai 21 a karkashin jagorancin Mawlavi Abdul Hakim, wani babban malamin mayakan, wanda kuma babban makusancin ne na shugaban Taliban Hibatullah Akhudzada.

Hakim ne ke shugabancin tsarin shari’a na kungiyar ta masu tsattsauran ra’ayin addini a yankunan da Afghanistan da Taliban ke iko da su.

Kakakin kungiyar ta Taliban Zabihullah Mujahid ya fadawa Muryar Amurka cewa “mun kafa kakkarfan ayari na sulhun na cikin gida na Afghanistan. Ya kumshi wakilan majalisar shugabanni ta Taliban ta Rehbari Shoura, yayin da aka nada babban alkalin alkalai na Taliban a zaman shugaban ayarin.”

Jami’ai sun ce bangarorin masu sulhun za su yi kokarin cimma matsayar samar da tsagaita wuta mai dorewa da kuma tsarin raba mukaman siyasa da za su shugabanci Afghanistan.

Shirin na samar da zaman lafiya ya samo asali ne daga yarjejeniyar da Washington ta cimma da Taliban a watan Fabrairu domin janye dakarun Amurka daga kasar, da kuma kai karshen yaki mafi dadewa na Amurka.

A halin da ake ciki kuma manzon Amurka na samar da zama lafiya a Afghanistan Zalmay Khalilzad, wanda ya rattaba hannun yarjejeniyar da Taliban, yana kan hanyarsa ta zuwa Doha domin soma shirin na kokarin somawar tattaunawar ta sulhu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG