Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Gina Tashoshin Manyan Motoci Na Zamani A Fadin Najeriya


Hukumar kasuwanci ta Teku da hukumar kiyaye hadura ta Najeriya, sun rattaba hannu akan yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin su domin kafa tashoshin tsayuwar manyan motoci a Najeriya.

Shugaban hukumar kiyaye haddura na Najeriya, Boboye Oyeyemi, yace hukumarsa zata horar da jami’ai, na hukumar kasuwancin jiragen ruwa kan yadda lasisi da rajistan manyan motoci yake domin gudanar da wannan aikin yadda ya dace.

Ya kara da cewa hukumar zata duba lafiyar manyan motocin domin suke jigilar kashi tasa’in cikin dari na kayan masarufi a dukkan fadin Najeriya.

Idan wannan yarjejeniya ta fara aiki gadan gadan inji shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa Malam Hassan Bello, za a ga cewa duk inda suke babu irin kazantar da aka saba gani kuma za a samarda mahimman abubuwan da suka dace kuma tuni wasu Gwamnoni sun fara yunkurowa.

Zaa yi amfani da naurori domin ganin duk inda manyan motoci suke da daukar matakin da ya dace idan suka tsaya a inda bai dace ba. Makon gobe duk masu ruwa da tsaki na wannan tashoshi zasuyi taro a Legas, domin Karin bayani akan wannan aikin dake da nasaba da raya tattalin arziki da zamanantar da harkokin mayan motoci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG