Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce duk wani harin da sojojin Amurka za su kai wa Iran, zai zama kwatankwacin harin da aka kai akan matatun man fetur din Saudiyya ne.
Yayin da yake magana da manema labarai a safiyar jiya Litinin, a kudancin farfajiyar fadar White House, an tambayi Shugaba Trump kan kalaman da Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya yi na dora laifin harin na Saudiyya akan Iran, sai ya ce, "ina ganin muna da ra’ayi iri daya, muna kokari ne kawai mu gano gaskiyar lamarin. "
Shugaban ya kara da cewa za’a san wanda ke da alhakin kai harin "nan da dan kankanin lokaci mai zuwa."
A yammacin jiya, Trump ya fadawa manema labarai a Ofishin fadar White House, a yayin ganawarsa da yarima mai jiran gado na Bahrain, Salman bin Hamad bin Isa Al Khalifa, cewa, duk da ba sa son yin yaki da Iran, "Amurka a shirye ta ke sosai", akan duk wani rikici, fiye da kowace kasa.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum